1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar PDP na cikin matsala

January 24, 2011

Jam'iyyar PDP a Najeriya na fuskantar gagarumar ɓaraka ta ficewar wasu daga cikin 'ya'yanta bisa abinda suka kira rashin adalci

Hoto: AP

PDP cikin tsaka mai wuya

A Najeriya Jam'iyyar PDP mai mulki na cigaba da fuskantar yayinda babban zaɓen da za'a gudanar a watan Aprilu ke ƙara gabatowa. Wannan dai ya biyo bayan matakan da jam'iyyar ta ɗauka ne na soke zaɓɓukan fidda gwani na 'yan takarar gwamna a jihohin kano da Kogi. A Jihar Kano magoya bayan tsohon gwamna Rabi'u Musa kwankwaso wanda shine ya lashe zaɓen fidda gwani da aka gudanar tun da farko sun yi barazanar marawa jam'iyar CPC baya a zaɓen shugaban ƙasa idan har jam'iyar ta hana shi tsayawa takara a zaɓen mai zuwa.

Shugaba Jonathan Goodluck.Hoto: AP

Fargaba da zaman zulumi

A waje guda kuma jama'a na cikin zulumi da fargaba sakamakon taɓarɓarewar tsaro da kuma halin rashin tabbas game da abinda za'a fuskanta a zaɓen mai zuwa ganin yadda yan siyasa idanunsu suka rufe suna neman mukamai ko ta wane hali.

Kira daga shugabannin addinai

Malamn addinin musulunci dana Kirista sun buƙaci gwamnati ta tashi tsaye domin magance wannan matsala kafin a jefa ƙasar cikin mawuyacin hali.

Ana iya sauraron sautin rahotannin wakilan mu Aminu Abdullahi daga Sokoto da Babangida Jibril daga Kano da kuma Al-Amin Sulaiman Mohammed daga Gombe a game da halin da ake ciki a siyasar ta Najeriya.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala
Edita : Mohammad Nasir Awal