Najeriya: PDP ta mika takarar shugabanci kudanci
August 26, 2025
Bayan kwashe makonni ana fadi tashi a tsakanin gwamnaonin jam'iyyar ta PDP da shugabanin jam'iyyar, taron majalisar zartaswar jam'iyyar karo na 102 da suka gudanar a Abuja, inda yayan jam'iyyar suka amince da daukan wannan mataki bisa gagarumin rinjaye da masu alamar lemar suka dauka. Wannan ya tabbatara da hasashen da ake yi na fara yin tayi da ma tuntubar tsohon shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan don ya zama dan takarar neman shugabancin Najeriya domin daga yankin kudancin Najeriya ya fito.
Karin Bayani: Atiku ya raba gari da PDP
Ficewar da tsohon mataimaki shugaban Najeriyar Atiku Abubakar ya yi daga jam'iyyar wanda tun bayan da aka kayar da jam'iyyar a zaben shugaban Najeriya a 2015 shi ne ke mata takara, lamarin da ya haifar da rigingimun cikin gida na jamiyyar ta PDP, domin wasu yayanta sun nuna harzuka da ya sanya su ficewa daga jam'iyyar, saura kuma suka yi mata kafar ungulu inda suka yi tsayuwar gwamin jaki kafarsu daya a jami'yyar daya kuma a wasu jam'iyyu musamman APC.
Tun kafin daukan wannan shawara dai gwamnonin jamiyyar ta PDP sun ta gudanar da tarurruka da ya kai su jihohi da dama a kokari na yiwa jamiyyar saiti. Wannan dai shi ne mataki na karshe kafin babban taron jamiyyar da za a gudanar a garin Ibadan na jihar Oyo.
Babbar jamiyyar adawar Najeriya ta PDP na kamala shirye-shiryen babban taron ja miyyar da zai zabi sabbin shugabanni duk da tabbatar da shugabancin da ta yi wa Umar Iliya Damagum a matsayin shugabanta bayan kwashe lokaci ana takadama a kansa bisa kalon yana samun goyon bayan minsitan Abuja Nyesom Wike da ake tababa a kan biyayyarsa ga jamiyyar da ya raba kafa.