1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: The Greens na nema wa kanta mafita

September 26, 2024

Bayan gaza samun nasarar a zabuka da dama da suka gabata, shugabannin jam'iyyar masu rajin kare muhalli ta Jamus wato the Green sun sanar da murabus din baki dayan majalisar gudanarwar jam'iyyar.

Jamus | The Green | Shugabanni | Murabus | Omid Nouripour | Ricarda Lang
Shugabannin jam'iyyar the Green ta Jamus, Omid Nouripour da Ricarda LangHoto: Kay Nietfeld/Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Da yake bayyani yayin taron manema labaran da suka gudanar domin bayyana murabus din nasu, shugaban jam'iyyar ta masu rajin kare muhalli ta Jamus wato the Green Omid Nouripour Ya bayyana godiya kan damar da aka ba su ta yin jagorancin. Ya kara da cewa sun dauki wannan matakin ne, bayan doguwar tattaunawa da ta sanya suka yanke hukuncin cewa akwai bukatar sauya shugabancin domin fara sabon lale. Nouripour ya nunar da cewa, hakan na nufin akwai bukatar jam'iyyar ta shirya sabon zabe na shugabanninta. Ita ma dai a nata bangaren abokiyar shugabancin Nouripour din wato Ricarda Lang ta nunar da cewa, akwai bukatar sababbin fuska a shugabancin jam'iyyar da ke rajin kare muhalli wato the Green din. Lang ta ce ba abu ne mai sauki ba gare su, amma sun cimma wannan matsaya domin samar wa jam'iyyar sabuwar makoma. A cewarta jam'iyyar tana bukatar hakan, domin samun mafita a zaben majalisar dokokin Jamus wato Bundestag da za a gudanar a shekara mai zuwa. Jam'iyyar ta masu rajin kare muhali ta gaza katabus a zabukan da aka gudanar a Jamus din na baya-bayan nan, abin da ya tilasta shugabancin the Green din daukar wannan mataki domin fatan tsira.