Jam'iyyun adawa a Turkiyya sun yi hadaka
May 5, 2018Talla
Hadakar jam'iyyun mai suna Nation Alliance ta rabawa manema labarai wannan sanarwa ce a yau Asabar jim kadan bayan cimma yarjejeniya tsakaninsu, sanarwar ta kara da cewar wannan shine matakin da zasu dauka don ganin kasar ta rabauta da sabon shugaban kasa.
Tun da fari jam'iyya mai mulki ta shugaba Erdorgan ta hade da wa su manyan jam'iyyu biyu a kasar inda suka yiwa kundin tsarin milkin kasar wata kwaskwarima da ta karawa shugaban kasar karfin iko, lamarin dake cigaba da samun suka daga bangarori daban daban.
Shugaba Erdogan dai ya bukaci gudanar da zabubbukan kasar shekara guda gabanin wa'adi.