Jam'iyyun Isra'ila na kokarin kafa gwamnati
April 26, 2020Talla
Nan gaba ne dai 'yan jam'iyyar ta Labor su kimanin dubu uku da dari takwas za su kada kuri'unsu kan wannan kuduri don sahalewa jam'iyyar shiga kawance da jam'iyyar Likud din da nufin gika gwamnati da ka yi ta kokarin yin a baya amma aka gaza samun nasara.
Jam'iyyar wadda a baya kurarta ta yi kuka a fagen siyasar kasar yanzu haka tana fuskantar koma-baya, inda a halin da ake ciki kujeru 'yan majalisar shidda kawai take da su daga cikin kujeru 120 da ake da su a majalisar dokokin isra'ila din.