1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus a hukumar kare hakkin yan Adam ta MDD

February 25, 2013

A karo na biyu, Jamus ta sake samun wakilci a hukumar kare hakkin 'yan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya

Hoto: Reuters

Wakilan Jamus sun shiga jerin kasashen da suka halarci zaman taron farko na hukumar kare hakin yan Adam ta majalisar dinkin duniya a birnin Geneva. Hukumar ta majalisar dinkin duniya tana da wakilcin kasashe 47 ne a cikinta. A bayan wakilcin ta na farko tsakanin shekarata 2006 zuwa 2009, Jamus karo na biyu kenan da aka zabe ta a hukumar ta kare hakkin yan Adam.

Sake zaben Jamus da aka yi a hukumar ta kare hakkin yan Adam ba al'amarine da kasar ta sameshi cikin ruwan sanyi ba. Wannan nasara tazo ne bayan kampe mai tsanani da aka samu tsakanin sauran kasashe na rukunin nahiyar Turai da suka nemi kujerar nahiyar, to sai dai tun a wa'adin ta na farko, Jamus ta taka rawar gani, abin da ya zama mai muhimmanci a takarar da tayi yanzu. Hanns Schumacher wakilin Jamus a ofishin majalisar dinkin duniya a Geneva yace gagarumin rinjayen da ta samu a lokacin kada kuri'ar zaben kasar da zata wakilci Turai, wata alama ce ta amincewa da matsayin Jamus da kasancewarta mai shiga tsakani da neman daidaitawa tsakanin dukkanin yankunan duniya.

To sai dai Darektar ofishin kungiyar kare hakin yan Adam ta Human Rights Watch a Geneva, Julie Riviero tace bai kamata a dauki sake zaben Jamus da aka yi a kujerar Tuirai a hukumarta kare hakkin yan Adam a matsayin abin da ya samu saboda aiyukan yan diplomasiyar Jamus a hukumar kawai ba. Jamus ta cancanci wannan kujera, kuma babu shakka zata hada kanta da sauran kasashe a hukumar domin duba al'amuranda suka shafi kare hakkin yan Adam a ko ina cikin duniya.

Shugaban Jamus, Joachim Gauck gaban taron hukumar kare hakkin yan Adam ta MDDHoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

Tace muna bukatar ganin Jamus ta maida hankalinta ga nazarin halin da ake ciki na kasa da kasa a hukumar ta kare hakkiny an Adam. Muna bukatar ganin Jamus din ta fita daga manufofinta na maida hankali kan al'amura masu daukar hankali kawai a gareta, kamar misali batun samarda ruwa mai tsabta ko kare muhalli ko fataucin jama'a. Ko da shike duka wadannan al'amura ne masu muhimmanci, amma muna bukatar samun yanayin da hukumar zata rika yanke kudiri kan sauran al'amuran da suka shjafi kare hakkin yan Adam, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Gwajin farko a game da hakan kuwa, zai samune idan aka zo duba batunkasar Syria Tun bayan barkewar rikicin kasar, Rasha da China suke ci gaba da toshe duk wani yunkuri da hukumar kare hakiny an Adam take yi na aikewa da sakon rashin jin dadi zuwa ga shugaba Bashar al-Assad. Duka kasashen biyui a shekara ta 2013, basu da wakilci a hukumar ta kare hakkin yan Adam.

Yanzu dai hukumar tana iya samun damar kasancewa mai baiwa kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya gargadi tun da wuri a kan batun keta hakkin yan Adam a wata kasa, tun kafin hakan ya faru, inji Beate Rudolf, darektan cibiyar kare hakkiny an Adam a Berlin.

Shugaban hukumar kare hakkin yan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Navi PillayHoto: AP

Tace hukumar tana iya maida hankalin ganin cewar idan a wata kasa aka lurada alamun keta hakkin yan Adam, nan da nan hukumar ta gabatar da kudiri, kuma cikin gagawa a kafa kwamiti da zai yi bincike a klasar da abin ya shafa, yadda sakamakon da za'a samu, zai baiwa kwamitin sulhu damar matsa lamba ga wannan kasa.

Kungiyoyin kare hakkin jama'a masu zaman kansu a Jamus sun yi kira ga hukumar ta majalisar dinkin duniya ta kara matsa lamba kan kasashe kamar Syria da Korea ta arewa da Myanmar. Jamus, inji kungiyoyin, kamata yayi tayi amfani da karfinta a hukumar, domin ganin wadannan kasashe basu ci gaba da take hakkin al'ummarsu ba.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Saleh Umar Saleh