Jamus a matsayin mai yin sulhu a Gabas Ta Tsakiya
February 6, 2012Saɓanin Amirka, Jamus ta sami aminci da yarda a tsakanin Israila da Falasɗinawa, sai dai manazarta na ganin cewa ƙasar ta Jamus na yin ɗari-ɗari wajen nuna tasirinta a shirin samar da zaman lafiya.
Tsawon shekaru da suka wuce Jamus ta yi ƙoƙarin gina dangantakar aminci da Falasɗinawa ba tare da ta mayar da Isra'ila saniyar ware ba. Ko da yake an ga yadda a 'yan shekarun nan sha'awarta akan Falasɗinawa ke ƙara yin ƙarfi. A shekarar bara kaɗai fadar mulki a Berlin ta baiwa hukumar gudanarwar Falasɗinawa gudunmawar tsabar kuɗi har euro miliyan 149. Bugu da ƙari a baya bayan nan gwamnatin ta sami amincewar al'umar ƙasa na miƙa waɗannan kuɗi ga hukumar gudanarwar Falasɗinawa wanda gwamnatin Israila ba ta so hakan ba.
Jim kaɗan kafin ziyarar sa zuwa Israila, Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya yanke shawarar ɗaukaka matsayin ofishin wakilcin Falasɗinawa a Berlin zuwa matsayin babban ofishin jakadanci.
Bayan sukar lamirin ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas, wani batu da ya kasance a fagen muhawarar 'yan siyasa a nan Jamus shine sukar yadda Israila ke cigaba da gina matsugunan Yahudawa. A hirar da ya yi da wani gidan radio na nan Jamus Westerwelle ya fito ƙarara inda ya baiyana cewa:
"Da farko dai sun san matsayin Jamus akan manufar faɗaɗa matsugunan cewa ba mu amince da shi ba. Wannan mataki ne wanda baki ɗaya a ƙungiyar Tarayyar Turai muka tsaya a kai kamar yadda muka amince da martaba muradun Israila. Yayin da kuma ba za mu manta da cewa wajibi ne Hamas ta yi watsi da aƙidar tarzoma ba."
Manufar harkokin wajen Jamus ɗin dai yana adawa da masu tsatsauran ra'ayi daga ɓangarorin biyu inda yake fatan za'a sake farfaɗo da tattaunawar shirin wanzar da zaman lafiya.
Sai dai a cewar manazarta kamar Moshe Zimmerman, wannan hikima ba za ta cimma wata nasara ba. Shahararren masanin tarinhin ɗan ƙasar Israila kuma ƙwararren akan al'amuran Jamus ya yi kiran fayyace inda aka dosa a manufofin na Jamus.
"Ko da yake Netanyahu na cigaba da aikin faɗaɗa matsugunan tamkar dai babu wani abu da ya faru, adawar da Jamus ta nuna ba abu ne da zai sanya Netanyahu ya sauya manufarsa ba, kamar dai irin sukar da bata taka kara ta karya ba, da shugabar gwamnati Angela Merkel ta yi. Amma a haƙiƙa, babu wani ƙwaƙwarar ƙudiri dake fitowa ta ƙin nuna goyon bayan gwamnati gwamnatin Israila, wannan shine gazawar manufar gwamnatin Jamus."
Haka shi ma Mustafa Barghouti mai rajin cigaban dimokraɗiyya kuma sakatare janar na ƙungiyar Falasɗinawa yana ganin idan aka ɗauke matsalar cin hanci da kuma rigimar aƙidar addini tsakanin Fatah da Hamas, to lokaci na neman ƙurewa idan har ana so a cimma shirin zaman lafiya.
"Idan Jamus ta nuna azama a wannan ɓangare, na tabbatar dukkan ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai za su bada goyon bayan wanzuwar cigaba kuma ta haka Tarayyar Turai za ta ɗauki matsayi mai ƙarfi ta adalci ba tare da nuna fifiko ba."
Barghouti yace cigaba da gina matsagunan da Israila ke yi yau da gobe yana kawar da damar yin sulhu, saboda kuwa za'a wayi gari Falasɗinawa basu da wurin da za su kafa ƙasarsu. Gwamnatin Israila dai ba ta damu da dukkan wani suka da ake yi mata na fatar baka ba. A saboda haka wajini ne a ɗauki matakin sanyawa gwamnatin takunkumi da riƙe tallafi akan harkokinta na soji da kuma katse huldar tattalin arziki da ita.
"Kamar dai yadda James Baker ya yi a shekarar 1990 inda ya baiyanawa Israila cewa matukar ku ka cigaba da faɗaɗa gine-ginen Yahudawa, to za'a yanke wannan kuɗi daga tallafin da Amirka ke baku, wannan shine kaɗai lokacin da irin wannan matsin lamba ya yi tasiri."
Dukkanin su dai Bargouti da Zimmerman sun baiyana cewa wannan ba batu ne na adawa da manufofin Isra'ila ba, amma mataki ne da zai amfani ɓangarorin biyu na Israila da Falasɗinawa.
Mawallafa: Lewis Gropp/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal