Jamus ta karfafa matakan yakar Coronavirus
March 9, 2020Ministan lafiya na Jamus ya sanar da soke duk wani taron da jama'a suka haura mutum 1000 a wani mataki na hana yaduwar cutar Coronavirus. Minista Jens Spahn ya sanar da hakan a yammancin jiya Lahadi gabanin wani zaman taron da ya hada kan jiga-jigan gwamnatin kawance da ke shirya matakan kare tattalin arzikin kasar daga duk wata barazanar cutar ta coronavirus.
A daya bangaren kuma, rahotannin daga kasar Masar sun tabbatar da mutuwar wani Bajamushe da ke ziyara a kasar a sakamakon kamuwa da cutar, a yayin da a kasar Australiya kuwa, mutuwar wasu dalibai uku da suka kamu da cutar ta tilasta ma mahukuntan kasar rufe wasu makarantu.
Cutar da ta samo asali daga kasar Chaina ta bazu zuwa sauran yankunan duniya, kawo yanzu dai yankin Antartica ne ba a sami bullar cutar ba wadda ta kama mutum fiye da dubu dari da halaka kimanin 3,500 Jamus ce kasa ta biyar mai yawan mutanen da suka kamu da Covid-19 wato kasa ta biyu a nahiyar Turai bayan kasar Italiya da cutar ta fi barna.