Jamus: An jingine matakin dta aka dauka kan Jam'iyyar AfD
May 8, 2025
Hukumar leken asiri ta kasar Jamus, ta jingine matakinta na ayyana jam'iyyar nan ta masu ra'ayin rikau a matsayin mai matsanancin ra'ayi watau AfD, matsayar da ta bayyana a kanta a makon da ya gabata.
Jinginewar hukumar za ta ci gaba ne har sai kotu ta yanke hukunci kan korafin da AfD ta shigar.
Wannan dai wani bangare na ci gaba a cewar jam'iyyar ta AfD, wadda ake ganin tana da akidu masu tsauri ciki har da na kyama ga baki.
Matakin hukumar leken asirin Jamus din na bayyana jam'iyyar a matsayin mai matsananci ra'ayi, ya janyo suka ciki kuwa har da gwamnatin Donald Trump ta Amurka.
Wasu dai daga cikin 'yan majalisar dokokin Jamus, sun bukaci da haramta jam'iyyar kwata-kwata, saboda abin da suka kira da tabargazarta ga tsari na dimukuradiyyar kasar.