Hukumar Lafiya a Jamus ta sallami wasu mutane da aka killace
February 16, 2020Talla
Sakataren Lafiya na Jamus Thomas Gebhart, ya shaidawa manema labarai cewar gabanin sallamar mutanen sai da jami'an lafiya a Jamus suka tabbatar basa dauke da kwayar cutar wacce ta hallaka sama da mutane 1,600 a Chaina. Makwanni biyu dai matafiyan suka kwashe killace a wani sansanin sojin Jamus da ke dab da filin jiragen sama na birnin Frankfurt.
Jamus dai ta kasance kasa guda cikin kasashen Turai da aka samu akalla mutane 16 sun kamu da cutar duk kuwa da cewar har ya zuwa yanzu wadanda suka kamun basu shiga mawuyacin hali ba kuma babu asarar rai.