1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan zaben Firimiyan Thüringen

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 6, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki sakamakon zaben da ya bai wa Thomas Kemmerich na jam'iyyar FDP nasara a matsayin firimiyan jihar Thüringen.

Ministerpräsidentenwahl Thüringen - Thomas Kemmerich FDP
Thomas Kemmerich zababben firimiyan jihar ThüringenHoto: picture-alliance/dpa/M. Schutt

Shugabar gwamnati Angela Merkel ta bayyana hakan ne a yayin ziyarar da take a yanzu haka a Afirka ta Kudu, inda ta bukaci da a soke zaben tare da gudanar da sabo. A ranar Laraba ne dai aka zabi Thomas Kemmerich na jam'iyyar FDP ta masu sassaucin ra'ayin a matsayin firimiyan jihar ta Thuringia da ke gabashin Jamus, ranar kuma da shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ta ayyana da mummunar rana ga dimukuradiyyar kasar.

Tuni dai zanga-zangar adawa da zaben hadin gwiwar da jam'iyyar AfD ta barke a Jamus, abin da ake tunanin ya kan iya jefa siyasar kasar cikin halin ni 'yasu. A jawabinsa da ke zaman tamkar nade tabarmar kunya, shugaban jam'iyyar ta FDP ta kasa Christian Lindner ya nunar da cewa ya yi mamaki matuka kan tallafin da jam'iyyar AfD ta bai wa jam'iyyarsa har ta kai ga cimma wannan nasara.


A nata bangaren jam'iyyar AfD din ta bayyana cewa gaba ta kai ta, kamar yadda kakakin jam'iyyar na kasa Tino Chrupalla Federal ya fadi. A nasa bangaren, zababben firimiyan na jihar Thuringia da ya kasance dan jam'iyyar FDP Thomas Kemmerich ya nuna takaicinsa dangane da yadda zabensa ke ta shan suka daga bangarori dabam-dabam.
Tuni dai jam'iyyar SPD da ke cikin gwamnatin hadaka ta Merkel ta bukaci CDU ta nisanta kanta da wannan zabe. A baya dai jam'iyyar ta FDP na cikin gwamnatin hadakar Jamus, sai a shekara ta 2017 ne ta gaza kai bantenta, abin da ya janyo mata abin da masu iya magana ke cewa da kyar na sha ya fi da kyar aka kamani, domin kuwa tana da 'yan majalisa 80 kacal cikin 709 da majalisar dokokin Jamus din ta Bundestag ke da su.

Shugabar gwamnati Angela Merkel ta yi kira da a soke zaben ThüringenHoto: picture alliance/AP/J. Meyer/Pool