Mutane 698 sun mutu a yini guda da corona a Jamus
December 17, 2020Talla
Cibiyar bincike ta Robert Koch ta ce a cikin yini daya an samu mutane 698 wadanda suka mutu a sanadin cutar yayin da aka samu sama da mutane dubu 26 sabbin kamuwa. A yau aka shirya shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta tattauna ta hanyar bidiyo da jami'an kamfanin BionNTech na Jamus wanda bisa hadin gwiwa da Pfizer na Amirka suka fito da rigakfin coronar. Ana sa ran a cikin sabuwar shekara mai kamawa za a fara yin rigakfin na corona a Jamus.