1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Ana kada wa Scholz kuri'ar yankan

December 16, 2024

Idan har shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya gaza samun kuri'u 367 daga zaman majalisar na yau, zabe gabanin wa'adi ya wajaba ke nan a watan Fabrairu mai zuwa.

Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture-alliance

'Yan majalisa uku daga jam'iyyar adawa ta AfD mai kyamar baki sun lashi takobin zaben ci gaba da zaman Olaf Scholz a matsayin shugaban gwamnatin Jamus a kuri'ar yankan kauna da 'yan majalisar suka shirya kada wa gwamnatinsa a wannan Litinin.

A yayin da yake jawabi a gaban 'yan majalisar Olaf Scholz ya zargi jam'iyyar FDP da yi wa gwamnatinsa ta hadaka makarkashiya waddarugujewarta ta sabbaba kada kuri'ar yankan kaunar ta wannan Litinin. Amma shugaban ya tunasar da 'yan majalisar irin alheran da Jamusawa za su ci gaba da mora idan har ya yinasarar tsallake rijiya a kuri'arda za a kada da ma zaben gabanin wa'adi da ake saran gudanarwa a watan Fabrairu mai zuwa.

Jagorar jam'iyyar ta AfD a majalisar dokoki ta Bundestag Alice Weidel ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus, DPA, cewa 'yan majalisar jam'iyyarta sun yanke shawarar nuna gamsuwa da shugaban gwamnatin da ke ci a yanzu saboda ba za su amince Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnnati ba, bisa zargin cewa zai zama shugaba mai son zubar da jini.

Friedrich Merz shi ne shugaban jam'iyyar CDU, wadda za ta iya karbe mukamin idan har kuri'ar yankan kaunar ta yi tasiri a kan Olaf Scholz wanda dan jam'iyyar SPD ne.

Tarihin siyasar Jamus dai cike yake da irin wannan kuri'a ta yankan kauna wadda ake yi domin auna karbuwar shugaban gwamnati a tsakanin 'yan majalisa. A baya shugabanni irinsu Willy Brandt a shekarar 1972 da Gerhard Schröder a shekara ta 2005, sun rasa mukamansu sakamakon zaben gabanin wa'adi da aka yi bayan da kuri'ar yankan kauna ta kayar da su.