1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiJamus

Jamus: Babu bunkasar tattalin arziki a 2025

Abdullahi Tanko Bala
April 24, 2025

Jamus ta kasance daya tilo a tsakanin kasashen G7 da tattalin arzikin bai bunkasa ba shekaru biyu a jere, ta na kuma fuskantar shekara ta uku ba tare da ci gaba ba a 2025

Tattalin arzikin Jamus na fuskantar koma baya
Tattalin arzikin Jamus na fuskantar koma bayaHoto: dts Nachrichtenagentur/IMAGO

Gwamnatin Jamus ta rage hasashen ci gaban tattalin arzikinta inda ta ce ba zai sami bunkasa ba a 2025 tana mai nuni da tasirin manufofin cinikayya na shugaban Amurka Donald Trump.

Ministan tattalin arzikin Jamus mai barin gado Robert Habeck ya ce yiwuwar samun cigaban kasar mafi karfin tattalin arziki a turai kalilan ne bayan da ta shafe shekaru biyu a jere 2023 da 2024 tana fuskantar koma bayan tattalin arziki.

Jamus dai ita ce kasa daya tilo a cikin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki na duniya G7 wadda tattalin arzikinta ya kasa ci gaba tsawon shekaru biyu, ta na kuma kan hanyar shekara ta uku a 2025 ba tare da cigaban tattalin arzikin ba.

Tattalin arzikin na Jamus ya ragu da 0.3% a 2023 da kuma 0.2% a 2024

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW