Jamus: Jam'iyyar CDU ta sami karin tagomashi
June 7, 2021
Talla
Jam'iyar ta CDU karkashin sabon shugabanta Armin Laschet ta sami nasara da kashi 37 cikin 100 na kuru'un da aka kada a Saxony-Anhalt a ranar lahadi, yayinda jam'iyar AFD ke da kashi 21 cikin 100. Ita kuwa jami'iyar The Greens da ke kokarin shan gaban CDU ta sami kaso mai sanyaya gwiwa wato kashi 6 kacal cikin 100 na kuri'un.
Sakamakon zaben da aka samu a tsohuwar jihar ta gabashin Jamus wani kwarin gwiwa ne ga Laschet da ke son zama shugaban gwamnatin Jamus a zabe mai zuwa na ranar 26 ga watan Satumbar wannan shekarar.