Shekaru 75 da kai harin birnin Dresden
February 13, 2020Talla
An dai shirya kasaitacccen taro domin karrama wadanda suka rasu a lokacin harin. Masana tarihi sun ce mutane 25,000 suka mutu a barin wutar da ya gudana na tsawon kwanaki uku kacal.
Shugaban kasar zai bi sahun dubban mazauna birnin domin gabatar da jawabi kan mahimmancin zaman lafiya da ma hakuri da juna.
Tuni dai magajin garin Dresden din Dirk Hilbert ya jagoranci fara taron ta hanyar ajiye furani domin tunawa da dubban mutanen da suka mutu. A ranar Asabar da ke tafe ne masu kyamar baki za su gudanar da bore.