1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi na son kafa shari'a a Jamus

August 4, 2020

Burinsu shi ne kafa shari'a a Jamus, suna kuma son cimma wannan buri cikin ruwan sanyi. Yaya halastacciyar akidar Islama take da hukumomin tsaron Jamus ke nuna damuwa da ita?

Prozess um Scharia-Polizei
An taba samun wasu da suka yi wa kansu lakabi da "'yan sandan shari'a" a JamusHoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

Yanzu fafayen bidiyo na masu dauke da manyan bindigogi suna aikata ta'asa sun kau daga labarai. Sai dai yanzu hukumomin na Jamus na sanya ido kan wani sabon salo na masu akidar Islama, wato sanya dokokin Muslunci cikin harkokin siyasa don bai wa addinin damar samun gindin zama a zamantakewar al'umma. Ko wadannan mutane na zama barazana ga Jamus?

A cikin shekarun 1990 aka kafa gamayyar Furkan a kasar Turkiyya, sannan a shekarun baya-bayan nan ta kafa rassa a birane da dama na Jamus ciki har da Hamburg da Dortmun da kuma Munich. Cenk Göncü shi ne shugaban gamayyar ta Furkan. "Muna son mu fayyace gaskiya da karya bisa dokoki na Al-Kur'ani. Muna aiki ne da koyarwar Annabi  Mohammad SAW."
Furkan na son cimma wannan buri cikin lumana, sai dai ba ta girmama tsarin zamani na dimukuradiyya. Ga misali tana son yin aiki hukunce-hukunce kamar yadda yake cikin Al-Kurani, misali datsa hannun barawo. Gamaiyar ta Furkan dai na goyon bayan manufar nan da ake wa lakabi da "Halastacciyar akidar Islama".

An haramta dabi'ar raba Al-Kur'ani kyautaHoto: picture alliance/dpa/J. Stratenschulte

Akwai hadari cikin tafiyar

To sai dai hukumomin kare kundin tsarin mulkin Jamus, sun yi imani cewa kungiyoyi da ke wannan da'awa na son su yi amfani da hanyoyi na lumana domin sauya tunanin al'umma su cimma burin kafa tsarin Musulunci mai dorewa, kamar yadda shugaban kotun kare kundin tsarin mulki a jihar NRW Burkhard Freier ya nunar: "A ganinmu wannan manufa ta "halastaciyyar akidar Islama," ta fi akidar Salafiyya ko tsattsauran ra'ayi hadari. Domin wannan manufar na kokarin kutsawa cikin al'umma ta kuma yi kane-kane ta samu angizo cikin siyasa da zamantakewar al'umma."

Kafafan yada labarun Jamus na SWR da ke yankin Kudu maso Yamma da BR ta jihar Bavariya da suka yi wannan bincike, sun yi hirarraki da jami'an kare kundin tsarin mulki na tarayya da na jihohi, da suka ce wannan manufa na da mambobi dubu 13.

Mathias Rohe masanin kimiyyar addinin Islama a JamusHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Mathias Rohe masanin kimiyyar addinin Musulunci ne, kuma a ganinsa akwai babbar matsala, amma ya yi kira da a guji yi wa Musulmi gaba daya kudin goro. "Idan ga misali muka yi amfanin da kalmar Shari'a a matsayin abin tuhuma, to ina ga mun ce makadi da rawa. Domin Shari'a ka iya zama salla ko azumi. Wato amfani da 'yancin yin addini. Saboda haka kullum ina neman karin bayani game da ainihin abin da suke nufi."

Alaka da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi?

Wani abin da ake takaddama a kansa shi ne, na gamayyar Musulmin Jamus da ta dukufa wajen shiga tattaunawa da Majami'u da kuma 'yan siyasa a Jamus. Sai dai masu kare kundin tsarin mulkin, na alakanta gamaiyar da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi. Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin gamaiyar ta Muslmin Jamus ya ci-tura, sai dai a rubuce karara ta ce baba alaka tsakaninta da 'yan uwa Musulmi, ta kuma yi fatali da kokarin saka ta cikin kungiyar.

Kafafan yada labaran Jamus na SWR da ke yankin Kudu maso Yamma da BR ta jihar Bavariya ne suka yi wannan bincike.