Jamus da Amirka na hanƙoron farfaɗo da shirin zaman lafiyar GTT
January 5, 2007Talla
SGJ Angela Merkel da shugaban Amirka GBW sun yi alkawarin ba wa juna cikakken hadin a kokarin warware rikici tsakanin Isra´ila da Falasdinawa. Merkel ta jaddada bukatar dake akwai wajen shirya taron bangarorin nan 4 da suka hada da KTT, MDD, Rasha da Amirka, dake tattaunawa da nufin samar da wata taswirar zaman lafiya a yankin GTT. A gun ganawar da suka yi a birnin Washington, shugaba Bush ya yi kyakkyawan fatan cewa za´a warware rikicin tsakanin Falasdinu da Isra´ila.
Shugabannin biyu sun kuma tattauna game da shirin nukiliyar Iran da halin da ake ciki a kasashen Iraqi da Afghanistan sai kuma batutuwan da suka shafi manufofin makamashi da cinikaiya.