1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Amirka na sake nazartar Siriya

Yusuf Bala Nayaya
August 27, 2018

A bayanin da ya yi Steffen Seibert da ke magana da yawun gwamnatin Jamus ya ce an ja hankalin Rasha ta gargadi gwamnatin Siriya kan halayyar da take nunawa don kauce wa ci gaban tabarbarewar lamura a Siriya.

Angela Merkel und Donald Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler/R. Sachs

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaba Donald Trump na Amirka sun nuna juyayinsu kan halin da ake ciki a Siriya musamman halin da al'umma suke ciki a yankin Idlib. Mai magana da yawun Angela Merkel ya ce shugabannin biyu sun nunar da hakan ne sa'ilin wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho.

A bayanin da ya yi a wannan yammaci Steffen Seibert ya ce an ja hankalin Rasha ta gargadi gwamnatin Siriya kan halayyar da take nunawa don kauce wa ci gaban tabarbarewar lamura a Siriyar.

Har ila yau Seibert ya kara da cewa shugabannin biyu sun kuma tattauna kan Ukraine da yammacin Balkans da harkoki na kasuwanci, sai dai bai yi karin haske ba kan wannan.