1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jamus da Faransa da Poland za su ci gaba da taimakon Ukraine

Suleiman Babayo MA
March 15, 2024

Bayan wata baraka da ake ganin an fuskanta yanzu kasashen Jamus da Faransa da Poland sun tabbatar da matakin ci gaba da taimakon kasar Ukraine domin kare kanta daga kutsen Rasha.

Ukraine-Krieg - Hilfskonvoi
Hoto: Matthias Rietschel/dpa/picture alliance

A wannan Jumma'a, Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya karbi bakuncin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Firaminista Donald Tusk na Poland, inda duk suna nuna cewa kai na hade wajen taimakon Ukraine a yankin da take fuskanta na mamaya daga Rasha. Lokacin da yake jawabi sakamakon taron Shugaba Macron na Faransa ya ce kasashen da suke taimakon Ukraine ba za su yi duk wani abin da zai tabarbara yakin da ke faruwa ba.

Kasashen uku sun ce za su tabbatar an yi duk abin da ya dace domin Ukraine ta kare kanta yadda taje bukata daga hare-haren dakarun Rasha, an yi taron tsakanin shugabannin kasashen uku a birnin Berlin na Jamus sakamakon yadda ake ganin sabanin da aka samu kan tallafawa Ukraine, don ci gaba da kare kanta daga mamayar da Rasha.