Jamus da Faransa na nazarin kafa rundunar tsaron Turai
August 29, 2025
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, na wani taro na musamman a wannan Juma'a, a yankin Riviera na Faransa mai gabar ruwa, don tattauna muhimman batutuwa kan sha'anin tsaro da tattalin arziki.
Taron zai samu halartar ministoci goma-goma daga kasashen biyu, irinsa na farko tun bayan darewar Mr Merz kan karagar mulkin Jamus, bayan da shugabannin biyu suka hadu jiya Alhamis a wurin shakatawar Mr Macron na Fort de Brégançon.
Karin bayani:Yaya ci gaban kasashen Afirka renon Faransa?
Sauran lamuran da shuabannin biyu za su nazarta har da batun kera makamai a kasashen Turai da shimfida tsarin kaddamar da rundunar tsaro ta hadin gwiwa a Turai.
Alaka tsakanin Jamus da Faransa ta jima tana wakana, inda aka sake dabbaka ta a zamanin mulkin shugaban gwamnatin Jamus da ya gabata Olaf Scholz da Mr Macron.