Jamus da Oman na yunkurin sansanta rikicin Isra'ila da Iran
June 15, 2025
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya tattauna da Sarkin Oman Sultan Haitham bin Tariq al-Said ta wayar tarho a wannan Lahadi, kan kokarin da ya kamata su yi, domin dakile fantsamar yakin Isra'ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.
Mr Merz ya gode wa sarkin bisa shiga tsakani da ya ke yi, a tattaunawar cimma masalahar kawo karshen shirin Iran na mallakar makamin kare-dangi na nukiliya, inda ya jaddada bukatar taka wa aikin birki.
Dukkan shugabannin biyu sun amince da tsoma baki cikin rikicin Isra'ila da Iran, don samar da sulhu a tsakaninsu, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Jamus Stefan Kornelius ya sanar.
Turkiyya da Rasha ma sun dauki irin wannan mataki, bayan da ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho ranar Lahadi kan wannan yunkuri, wanda suka hakikance cewa diflomasiyya ce kadai hanya tilo ta sasanta wannan rikici, da kuma batun takaddamar nukiliyar Iran.
Karin bayani:Shugaba Trump na Amurka ya gargadi Iran kan yaki da Isra'ila
Ita ko Burtaniya gargadi ta yi 'yan kasarta da su guji yin tafiye-tafiye zuwa Isra'ila don kare rayukansu, sakamakon barkewar wannan yaki.
Wannan na cikin sanarwar da ma'aikatar harkokn waje ta fitar a wanna Lahadi, tana mai karin hasken cewa yakin ka iya fadada cikin hanzari kafin a ankara, a don haka ne kasar ta dauki wannan mataki na rigakafi.
Kuma firaminista Keir Starmer ya amince da tura jiragen yaki zuwa Gabas ta Tsakiya, domin dakile fadadar yakin.