Jamus za ta taimakawa sake gina Siriya bayan yakin basasa
June 18, 2025
Talla
Wannan majalisa na da nufin tallafawa sake gina kasar bayan shafe fiye da shekaru goma ana yakin basasa.
Wadephul, wanda ya ce sun amince da matakin da takwaransa na Siriya Asaad al-Shaibani yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, ya ce ofishin kula da harkokin wajen Jamus zai gudanar da ayyukan majalisar.
Tun da farko dai babban jami'in diflomasiyyar na Jamus ya shirya kai ziyara birnin Damascus a ranar asabar da ta gaba, sai dai kaddamar da manyan hare-haren da Isra'ila ta yi a kan Iran a ranar Juma'a, ya tilasta masa dakatar da tafiyar.