1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Diflomasiyya ce mafita a yakin Ukraine

December 15, 2023

Shugaban tsagin jam'iyyar Social Democrate a majalisar dokokin Jamus Rolf Mützenich, ya bukaci amfani da sabbin dabarun diflomasiyya wajen warware yakin Rasha da Ukraine.

Hoto: Jens Krick/Flashpic/picture alliance

Shugaban tsagin jam'iyyar Social Democrate a majalisar dokokin Jamus Rolf Mützenich, ya bukaci amfani da sabbin dabarun diflomasiyya wajen warware yakin Rasha da Ukraine, tare kuma da jaddada goyon bayan Ukraine din.

A cewarsa ya kamata gwamnatin Jamus ta dauki matakin diflomasiyya a yakin Ukraine a tsare-tsare da manufofin gwamnatin Jamus na shekara ta 2024, tare kuma da tattaunawa da kasar China da kuma sauran kasashe wajen kawo karshen rikicin, kamar yadda ya yi karin haske a jaridar Rheinische Post.

Mützenich, ya ce kasashe irin su India da Brazil da Indonesia da sauran kasashen dake yankin na da  kima da mutunci a wajen Putin, adon haka akwai bukatar ayi amfani da damar wajen shawo kan Putin don kawao karshen yakin.

Ya kuma kara da cewa shugaban Rasha zai iya daukar lokaci mai tsawo ya na wannan yaki ba tare da gajiyawa ba, adon haka Jamus  na tare da Ukraine domin kare ta daga duk wata barazana.