Dokar amfani da kyalen fuska ta fara aiki a Jamus
April 27, 2020A daukacin kasar dai ciki har da nan birnin Bonn an soma aiki da dokar a yau din nan , sai dai dokar na da dan sassauci a wasu yankunan musamman a birnin Berlin inda duk da tilasta wa jama'a saka kyalen a wuraren sufrin jama'a, abin ba haka ayake ba a shagunan sayen kayayaki.
Sannan rahotanni sun ce akwai matakin ladabtarwa ga wadanda suka gujewa aiwatar da dokar inda a Jihar Bayern hukumomi ke iya cin mutun tarar da ta kai kimanin euro 150.
Wannan dai wani ne daga cikin wasu muhimman matakan da hukumomin kasar suke dauka na sakin mara ga dokar takaita zirga-zirga, inda kawo yanzu wasu shagunan suka kasance a bude baya ga matakin bude wasu makarantu a farkon watan gobe.
Ya zuwa yanzu fiye da mutn 5. 750 ne suka rasa ransu daga cikin fiye da dubu 155 da suka kamu da Corona a nan Jamus.