1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyara ga dokokin karbar fasfon Jamus

Pieper Oliver AS/LMJ/MTH
July 2, 2019

Hukumomi a Jamus sun kwaskware dokar zama dan kasa ga 'yan kasashen waje. Daga cikin gyaran fuskar da dokar ta samu har da batun sajewa sosai da al'adun 'yan kasar da batun alaka da ta'addanci da makamantansu.

Symbolbild Doppelpass / doppelte Staatsbürgerschaft
Fasfo din Jamus da na Turkiyya, ga masu son mallakar fasfo na kasashe biyuHoto: picture-alliance/blickwinkel/McPHOTO

Sabuwar dokar  dai ta nunar da cewa idan ya kasance an samu mutum da alaka da wata kungiya ta 'yan ta'adda to shakka babu zai rasa matsayinsa na dan kasa. To sai dai wannan ya ta'allaka ne kawai ga wadandan suke da fasfo na kaashe biyu, wato na Jamus da kuma na wata kasa ta daban. Wannan batu dai ya ja hankalin mutane da dama, sai dai masu ruwa da tsaki da ma 'yan siyasa sun ce wannan ba wani abu ne da ya kamata a tada jijiyar wuya a kansa ba. Farfesa Daniel Thym na jami'ar Konstance kana kwararre kan dokokin shige da fice da kuma na bakin haure na daga cikin masu wannan ra'ayi.


Ya ce: Na yi mamakin yadda ake zazzafar muhawara kan wanann batun. Dokar ta fi mayar da hankalinta ne kan matsaloli guda biyu, wanda ko kusa ba za su sauya matsayin wadanda suka jima suna zaune a Jamus ba."

Wani abu har wa yau da sabuwar dokar ta kunsa shi ne batun sajewa da al'adun Jamus. Dokar dai a halin yanzu ta hana bayar da takardar zama dan kasa ga duk wanda ke da mace fiye da guda, kasancewar auren mata biyu ko fiye da haka ya saba da al'adar Jamusawa. Jama'a da dama da ma 'yan siyasa na kasar ciki kuwa har da Auch Linda Teuteberg da ke zaman 'yar majalisa kana sakatariyar jam'iyyar FDP na ganin ba ma abu ne da za a yi wata muhawara a kansa ba kasacewar a al'adance Jamusawa basa auren mace fiye da guda.

Tantance masu son karbar takardar zama dan kaa da kuma fasfo na JamusHoto: AP

Baya ga wannan batu, akwai kuma maganar rage yawan shekarun da mutane ke bukatar yi a kasar kafin ya samu 'yanci mika takarsunsa da nufin neman ya zama dan kasa. A baya dai shekarun na kamawa ne daga biyar zuwa takwas amma yanzu ana kokarin mayar da su zuwa 10, wanda hakan ya janyo cece-kuce. Wannan ne ma ya sanya wasu 'yan siyasar ke ganin an tsaurara sannan bijiro da zance a lokacin da galibin mutane ke tafiya hutun bazara ma wani abu ne da ake ganin bai dace ba, domin galibin wadanda za su zauna don tattaunawa kan batun sun tafi hutu kamar yadda Aziz Bozkurt na jam'iyyar SPD ya nunar.

Ya ce: "In da ni ne rage tsaurin abin zan yi, idan gaba-gadi aka zabi irin abubuwan da za a mayar da hankali a kansu. Ban san dalilinsu ba amma dai akwai wasu mutanen da ke gujewa tattaunawa kan wannan batu a baya amma yanzu an tado da shi. Wannan abu fa ba zai samar wa tsarin demokradiyyarmu makoma mai kyau ba."

Yanzu haka dai masharhanta na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu, inda wasu ke cewar hakan zai taimaka wajen tsaftace tsarin bayar da takardar zama dan kasar ga bakin da ke Jamus, yayin da wasu ke cewar sababbin matakan ba za su haifar da wani abu ba illa tallafawa masu kin jinin baki a kokarinsu na ganin 'yan kasasahen ketare ba su samu damar zama Jamusawa ba.