Jamus: Dole a bai wa Falasdinu 'yanci
March 27, 2018Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya sake jaddada matsayin Jamus kan samar kasashe biyu masu cikakken 'yanci, a matsayin abu mafi a'ala ga dorewar zaman lafiya a rikicin Isra'ila da Falasdinawa. Mr. Maas ya fadi hakan ne a jiya Litinin a wata ganawar da ya yi da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da kuma ministan harkokin wajen Falasdinu a Ramallah.
Ministan na Jamus ya bukaci gwamnatin Falasdinun ta yi la'akain sanya Amirka a tattaunawar zaman lafiya da za a yi, saboda wuyar cimma nasara, muddin aka ware Amirkar. Amma fa shugaban Falasdinawan Mahmoud Abbas, ya yi watsi da shiga tasakanin Amirkar, musamman ta la'akari da ayyana birnin Kudus da shugaba Donald Trump ya yi cikin watan Disamabar bara, a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila.
Su dai Falasdinawan na cewa ne gabashin birnin na Kudus shi ne zai kasance fadar gwamnatin da suke da'awar kafawa, koda yake shugaban na Falasdinawa ya yaba muhimmancin kasancewar Jamus da kungiyar EU a shirin samar da zaman lafiya tsakaninsu da Isra'ila.