1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar tsohon jami'in Siriya a Jamus

Matthias von Hein SB/LMJ
January 12, 2022

Wata babbar kotu da ke birnin Koblenz na Jamus, za ta bayyana matsaya kan tsohon babban jami'in Hukumar Leken Asirin Kasar Siriya da ake zargi da ganawa mutane azaba a yakin basasa da Siriyan ta tsinci kanta a ciki.

Jamus | Shari'ar azabtar da mutane a Siriya
Anwar R. a gaban kuliya, kan tuhumar cin zarafin dan AdamHoto: Thomas Frey/dpa/picture alliance

Shi dai wannan babban jami'i Kanar Anwar R. zai fuskanci zaman gidan fursuna, sakamakon shaidun da aka gabatar a kansa. Ofishin mai shigar da kara na gwamnatin tarayya a Jamus, ya gabatar da karar da ke zama ta farko a duniya kan cin zarafin dan Adam karkashin tsarin kasar Siriya da ake yakin basasa. Jean Amery wadda ta tsira daga sansanin gwale-gwale, ta zargi tsohon jami'in leken asirin Kanar Anwar R. da halaka fiye da mutanen 30. Akwai zargin cin zarafi fiye da 4000. Wolfgang Kaleck wanda ya kafa Cibiyar Kula da Tsarin Mulki da Kare Hakkin dan Adam ta kasashen Turai, shi ne ke wakilatar 'yan Siriya da aka ganawa azaba a wannan shari'a da ke wakana a Jamus: "Matakin karshe na babbar kotun da ke Koblenz, zai nuna cewa irin wannan matakin shari'a mai yiwuwa ne a Jamus. Wannan na nufin a ko'ina gwamnatin ta gallaza wa mutane, za a iya daukar matakin shari'a a kansa a Jamus. Gare ni wannan shi ne muhimmancin matsayin."

Ana zargin Anwar R. ta cin zarafi da take hakkin dan Adam yayin yakin SiriyaHoto: Thomas Frey/dpa/picture alliance

Masu gabatar da kara sun bukaci a yanke wa tsohon babban jami'in dan shekaru 58 a duniya hukuncin daurin rai-da-rai sakamkon shaidun da aka gabatar, inda fiye da mutane 60 suka ba da shaida. Ana dai zargin manyan jami'an gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta Siriya da gallaza wa mutane, musamman tun shekara ta 2011 bayan da kasar ta tsunduma cikin yakin basasa. Sai dai har yanzu kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam suna ganin ana nuna sassauci ga manyan jami'ai, ganin yadda tsohon jami'in Kanar Anwar R. shi da kansa ya balle daga cikin gwamnati ya taimaki fursunoni da ake ganawa azaba suka tsere sannan ya yi tafiya don radin kansa, inda ya tsere zuwa kasar Jordan a shekara ta 2012 daga Siriya. A cewar Fritz Streiff lauya mai kare hakkin dan Adam, manyan jami'ai na can sama ya dace a tuhuma. A daya bangaren Luna Watfa wadda take saka ido kan shari'ar tsohon jami'in Hukumar Leken Asirin ta Siriya da ake yi Jamus, ta ce tuni ya sauya gabanin yanke masa hukunci. Duk matsayin da kotun ta Jamus da dauka kan wannan shari'a, zai kara aika sako ga gwamnatocin da ke ci gaba da take hakkin dan Adam.