Tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da farmaki a kan kasar Iran, lamura suka rincabe a yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan a yanzu, ya zama gagarumin kalubale ga manufofin Jamus na kasashe waje.
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich MerzHoto: Thilo Schmuelgen/POOL/AFP via Getty Images
Talla
Jamus ta kasance mai taka tsan-tsan a kan manufofin yankin Gabas ta Tsakiya, amma yanzu kasar ta shiga mawuyacin hali sakamakon barkewar rikici tsakanin Iran da Isra'ila, bayan da Isra'ila ta fara kaddamar da farmaki a kan Iran. Tabbatar da tsaron Isra'ila na cikin bangaren manufofin kasar Jamus, kamar yadda tsohuwar shugabar gwamnati Angela Merkel ta jaddada lokacin da take rike da madafun iko. Shi ma magajinta Olaf Scholz ya karfafa matsayin, musamman bayan harin watan Oktoba na shekara ta 2023 da tsagerun 'yan Hamas na Falasdinu suka kai cikin Isra'ila. Ministan harkokin wajen Jamus na yanzu Johann Wadephul kuwa, na ganin sabon riki a matsayin zagon kasa ga tsaron Isra'ila.
Ruwan rokoki a Tel Aviv, rusau a Gaza - Rikici tsakanin Israila da Falasdinawa na kara yin kamari a 'yan kwanakin nan. Sai dai kamar kullum farar hula daga bangarorin biyu sune ke shan wuya.
Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images
Israila na kai harin ramuwar gayya
Barnar ba ta kare ba. Jiragen yakin Israila na luguden bama bamai a kudancin Gaza inda ta ke kai hari kan kungiyar Falasdinawa ta Hamas.
Hoto: Said Khatib/AFP/Getty Images
Isra'ila ta kira dakarun wucin gadi
Rundunar sojojin Israila na yin gangamin dakaru da tankokin yaki a kan iyaka da zirin Gaza lamarin da ke tunato da abin da ya wakana a yakin 2008 da 2009 da kuma 2014.
Hoto: Amir Cohen/REUTERS
Hudowar rana
Hayaki ya turnuke sararin samaniya a wannan Laraba a Khan Younis a yankin zirin Gaza. Tun a farkon mako rikici tsakanin Israila da Falasdinawa ya barke a bainar jama'a.
Hoto: Youssef Massoud/AFP/Getty Images
Neman tsira da rayuwa
A birnin Gaza, wadannan falasdinawan sun guje wa farmakin Israila a ranar Talata. Akalla ‘yan Israila takwas suka rasu yayin da ma’aikatar lafiya ta Falasdinawa ta ruwaito cewa akalla mutane 109 suka rasu run daga ranar Litinin.
Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images
Rusau a birnin Gaza
Israila ta ce ta kai hari kan gidaje kamar wannan a birnin Gaza, wanda ke dauke da ofisoshi na ‘yan kungiyoyin ‘yan bindiga ko kuma inda shugabannin tsagerun ‘yan Hamas ke zaune.
Hoto: Suhaib Salem/REUTERS
Harin rokoki a Tel Aviv
Kungiyar Hamas da ke mulki a zirin Gaza ta harba rokoki cikin Tel Aviv a daren ranar Laraba. Na’urorin kakkabo makamai masu linzami na Isrila suna bada kariya ga birnin tare da lalatawa ko kuma sake tankada makaman masu linzami zuwa sama yadda ba za su yi wani lahani mai yawa ba.
Hoto: AnAs Baba/AFP/Getty Images
Jira cikin kaguwa
Sai dai kuma na’urar kakkabo makaman masu linzami da ake kira “Garkuwar karfe“ ba ta samar da kariya dari bisa dari. Idan aka busa sarewa dukkan ‘yan Israila sai su bazama neman mafaka cikin gaggawa. Ko da kuwa da karfe uku ne na dare kamar wannan safiyar a nan.
Hoto: Gideon Marcowicz/AFP/Getty Images
Har yanzu akwai hadari
Ko da za a kakkabo rokokin Falasdinawa, baraguzai da ke fadowa suna da hadari. An lalata wani gida a wannan yankin Yahudawa da ke arewa da babban firin jirgin saman Israila. A cewar sojojin Israila Falasdinawa sun harba rokoki fiye da 1000 tun daga ranar Litinin.
Hoto: Gil Cohen-Magen/AFP/Getty Images
Hannu a Ka
Duk wanda bai iya samun mafaka akan lokaci ba, kan yi kokari bakin iyawarsa yadda zai tsira kamar wadannan mutanen a yankin Ashkelon da ke tazarar kilomita 10 daga arewacin zirin Gaza.
Hoto: Jack Guez/AFP/Getty Images
Duwatsu da gwangwanayen hayaki mai sa hawaye
A ‘yan kwanakin baya bayan nan ana ta samun gagarumar zanga zanga tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Israila a birane da dama, kamar nan birnin Hebron a yankin da Isriila ta mamaye a gabar yamma. Masu zanga zanga na ta jifa da duwatsu da sauran abubuwa.
Hoto: Hazem Bader/AFP/Getty Images
Hotuna 101 | 10
Jamus dai tana damuwa da abin da yake faruwa yanzu haka, kuma tana goyon bayan Isra'ila ta kare kanta da mutanenta. Ministan tsaron Isra'ila ya ce kasarsa ta dauki mataki a kan Iran saboda kandagarki, sakamakon zargin Iran da neman mallakar makaman nukiliya. Hans-Jakob Schindler masanin kan Gabas ta Tsakiya a Cibiyar Yaki da Matsanancin Ra'ayi, na ganin hanyar magance wannan rikici ita ce tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Duk da cewa Jamus tana goyon bayan Isra'ila, amma haka ba ya nufin duk abubuwan da gwamnatin Isra'ila ta yi daidai ne kamar yadda masana suka nunar. Kuma sabuwar gwamnatin Jamus karkashin shugaban gwamnati Fredrich Merz tana shirye ta soki wasu manufofin Isra'ila, fiye da gwamnatin da ta shude.