Jamus: Jam'iyyar CDU ta Merz ta yi rawar gani a zabe
September 14, 2025
Yayin da aka rufe rumfunan zabe a fadin Jihar North Rhine-Westphalia, jiha mafi girma a Jamus a zaben kananan hukumomi da na magadan gari, hasashen sakamakon farko ya nuna Jam'iyyar CDU ta shugaban gwamnati Friedrich Merz na shirin samun nasara, sai dai jam'iyyar kyamar baki ta AfD ita ma tana cikin shaukin murna.
Jam'iyyar CDU ta Merz ana sa ran za ta sami kashi 34 cikin dari na kuri'iun da aka kada, Sai Jam'iyyar SPD da ke biye mata da kashi 22.5 cikin dari sai kuma AfD mai kyamar baki da ke da kashi 16.5 cikin dari inda ta rubanya har sau uku sakamakon da ta sami na kashi 5.1 cikin dari a zaben 2020.
Zaben na wannan lahadin shi ne na farko da aka gudanar tun bayan da Friedrich Merz ya hau karagar mulki a matsayin shugaban gwamnati a watan Mayu.
AfD ta sami gagarumar nasara a shekarun baya bayan nan inda ta zama jam'iyya ta biyu mafi karfi a kasa baki daya. Ko da yake magoya bayanta sun fi karfi a gabashin Jamus amma ta na fatan motsawa a yammacin Jamusa.