Jam'iyyar SPD a Jamus na taro kan batun 'yan cirani
July 4, 2018Jam'iyyar SPD da ke kawancen masu mulki a nan Jamus ta sanar da amincewa a bisa manufa da yarjejeniyar da abokanan kawancanta na CDU da CSU suka cimma kan batun 'yan gudun hijira. Sai dai kuma ta ce za ta gudanar da taro tsakanin shugabanninta a wannan Laraba kafin bayyana matsayinta na karshe a kai.
Amma dai shugaban jam'iyyar ta SPD kana mataimakin shugabar gwamnati Andrea Nahles ya bayyana cewa yana kyautata zaton samun fahimtar juna da abokanan kawancan nasu kan batun 'yan gudun hijirar.
A jiya dai ne shugabannin jam'iyyun uku suka gudanar da taro a birnin Berlin domin cimma matsaya a tsakaninsu kan wannan batu na 'yan gudun hijira bayan da jam'iyyar ta SPD ta nuna shakkunta a game da yarjejeniyar da abokanan kawancan nata suka cimma a daren Litinin washe garin Talata wacce ta tanadi kafa wasu sansanonin karbar 'yan gudun hijira da kuma tantance su a kan iyakar kasar ta Jamus da makobciyarta ta Ostriya.