1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kotun Jamus ta yi wa wani daurin rai da rai

December 21, 2020

Wata kotu a Jamus ta yanke wa wani matashin Bajamushe mai ra'ayin kyamar baki Stephan Balliet hukuncin daurin rai da rai.

Magdeburg I Prozess zum Terroranschlag von Halle
Hoto: Hendrik Schmidt/dpa/picture alliance

Mai shari'a Ursula Mertens da ta bayar da hukuncin ta ce kotu ta samu matashin da laifin kisan mutane biyu a watan Oktobar 2019 a kokarinsa na nuna kyama ga Yahudawa a birnin Halle da ke gabashin Jamus.

Tun a watan Yuli na wannan shekarar matashin ya amsa laifinsa ya kuma ce tun da farko ya shiga wurin ibadar Yahudawa domin ya kashe gabadayan mutane 51 da ke ciki, amma sai ya hadu da tirjiya ya kasa cimma burinsa, ya buge da kisan mutane biyu. 

Hukumomi sun ce za su ci gaba da daukar matakan ladabtar da masu kyamar baki wadanda ke da ra'ayi irin na 'yan Nazi a Jamus.