1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Majalisa ta kada kuri'ar yankar kauna

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 16, 2024

Za a gudanar da sabon zaben kafin wa'adi a Jamus a ranar 23 ga watan Fabarairun 2025, maimakon watan Satumba da ya kamata a ce wa'adin gwamnatin ya kare.

Deutschland Berlin 2024 | Bundestag debattiert über 35 Jahre Mauerfall und mögliche Neuwahlen
Hoto: Christoph Soeder/dpa/picture alliance

Gwamnatin hadakar ta jam'iyyu uku da shugaban gwamnati Olaf Scholz ke jagoranta ta rushe ne, bayan da ministan kudi Christian Wolfgang Lindner dan jam'iyyar masu ra'ayin jari hujja FDP ya yi murabus sakamakon korar da Scholz ya yi masa daga mukamin. Tuni shi da wasu mambobin jam'iyyarsa suka fice daga gwamnatin, a daidai lokacin da kasar ke fama da dimbin bashi tare da barin takwarorinsa na SPD da Greens  cikin gwamnatin da ta kasance ba ta da rinjaye a majalisar dokoki.

A yayin da Jamus ke cikin tsaka mai wuyar tattalin arziki, rushewar gwamnatin ta tilasta Scholz bukatar majalisar ta kada masa kuri'ar yankan kauna. Yayin da yake jawabi a majalisar gabanin kada kuri'ar a wannan Litinin din, Scholz ya ce:

Karin Bayani: Rikicin siyasa ya kunno kai a gwamnatin Jamus

Hoto: Michele Tantussi/Getty Images

"Wannan shi ne karo na shida a tarihin Jamus da shugaban gwamnati ya nemi a kada masa kuri'ar amanna, a karkashin sashe na 68 na kundin tsarin mulkin kasar. Sau biyu wacce na gada ta nemi hakan, kana Willy Brandt da Helmut Kohl da kuma Gerhard Schröder duk sun yi amfani da wannan sashe waje neman a kada musu kuri'ar yankan kauna. Fatana shi ne yin zabe a Jamus, ta yadda al'ummar kasar za su zabi makomar siyasarsu. Wannan shi ne dalilin da ya sanya na bukaci a kada min kuri'ar yankan kauna a yau."

Sai dai shi da kansa Scholz ba shi da kwarin gwiwar tsallake wannan siradi, kuma majalisar dokokin ta Bundestag ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen fatattakarsa daga kan mukamin nasa kamar yadda shugabar majalisar dokokin Baerbel Baas ta bayyana sakamakon:

Karin Bayani: Shugaban kasar Jamus ya bukaci shugabannin siyasar kasar su kai zucciya nesa

Hoto: Christoph Soeder/dpa/picture alliance

"Ta ce: "Kuri'u 367 ake bukata kafin tsallake kuri'ar yankan kauna, sai dai kuma shugaban gwamnati bai samu kuri'un 'yan majalisa 367 da suka amince masa ba."

Scholz din ya samu goyon bayan 'yan majalisa 207 ne kacal cikin mambobi 733, yayin da 394 suka kada kuri'ar yanke masa kauna 116 kuma suka yi rowar tasu kuri'ar. Bayan kada kuri'ar dai Sholz ya samu kakkausar suka daga jagoran babbar jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin 'yan mazan jiya CDU Friedrich Merz wanda ke cewa:

Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

"Za ka bar mana kasar cikin gagarumin rikicin tattalin arziki a tarihinmu, karo biyu ne kawai Jamus ta taba samun kanta cikin masassarar tattalin arziki shekaru biyu a jere. Guda lokacin Gerhard Schroeder wanda ya gabatar da ajandar 2010, sai kuma karo na biyu lokacin Olaf Scholz kuma kana tsaye a gabanmu kana nuna mana komai na tafiya yadda ya kamata, kana bukatar mu sake karbo bashin da zai cutar da 'yan baya."

Karin Bayani:Ana neman mafita ga tattalin arzikin Jamus

Hoto: John MacDougall/Pool Photo/AP/picture alliance

A karkashin dokokin Jamus, in har aka kada kuri'ar yankan kauna ga shugaban gwamnati shugaban kasa zai rusa majalisar dokoki domin gudanar da sabon zabe bayan shugaban gwamnati ya bukaci a kada masa kuri'ar. Tuni kuma Sholz ya gana da Shugaba Frank-Walter Steinmeier kan wannan batu, inda Steinmeier ke da wa'adin kwanaki 21 ya rusa majalisar dokokin.