1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Ma'aikatan filayen jiragen sama za su tafi yajin aiki

January 30, 2024

Ma'aikata kimanin dubu ashirin da biyar da ke aiki a manyan filayen jiragen saman Jamus ake hasashen za su shiga yajin aikin bayan sun kasa cimma daidaito da hukumomi kan batun karin albashi.

Hoto: Michael Probst/AP/picture alliance

Ma'aikatan da ke aiki a sashen tsaro na manyan filayen jiragen saman Jamus za su tsunduma yajin aikin gama-gari domin neman karin albashi, inda wannan mataki ke kasancewa a fannin tattalin arziki na sufurin jiragen sama a nahiyar Turai.

Kungiyar ma'aikatan ta Verdi ta sanar da cewa mambobinta za su kauracewa aiki a filin zirga-zirgar jiragen sama mafi girma a Jamus da ke Frankfurt da kuma na Berlin babban birnin kasar har ma da wasu filayen jiragen sama guda tara  a sassa dabam-dabam na Jamus din.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce har yanzu ba a samu daidaito ba wajen fitar da matsaya kan karin albashi da hukumomin filayen jiragen saman Jamus, amma abin da suke bukata shi ne karin euro biyu da centi 80 kwatankwacin dalar Amurka uku a duk sa'a guda tare da samar da sauran kayan aikin da za su rage wa ma'aikatan radadin hauhawar farashi da ake fuskanta a kasar.