Jamus: Batun wajabta rigakafi na ja hankali
July 26, 2021A lokacin da take tofa albarkacin bakinta dangane da wannan batu, Ministar shari'ar Jamus Christine Lambrecht ta nuna adawa da matakin tilasta wa jama'a yin allurar rigakafin, tana mai cewar ba a jima da samun wadatarta ba a duniya.
A dangane da shawarar da ministan da ke kula da ayyukan fadar shugabar gwamnati Helge Braun ya bayar na daukar mataki akan wadanda suka ki yin rigakafin corona, minista Lambrecht ta ambato rashin yin allurar da hurumin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Wasu 'yan siyasa na son a iya amfani da dokar takaita walwalar jama'a don gindaya sharadin takardar shedar yin rigakafin corona a gabanin barin mutane su shiga gidajen cin abinci.
Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da alluran rigakafin corona suka yi karanci a kasuwannin duniya a cewar ministar shari'ar Jamus din.