Wadanda da suka kamu da cutar coronavirus ya ragu a Jamus
April 6, 2020Wannan dai shine karo na hudu a jere da ake samun raguwar wadanda suka kamu da cutar a Jamus kamar yadda alkaluma da cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa ta Robert Koch suka nunar a wannan Litinin.
Tun daga farko a ranar Lahadi Jami'ar Johns Hopkins ta Amirka ta ce kasar Jamus ta doshi adadin mutun dubu 100 da suka kamu da kwayar cutar Covid-19 a yanzu haka, a yayin da ta ke wallafa wani binciken da ta gudanar.
Rahoton ya ce adadin wadanda suka gamu da ajalinsu sakamakon cutar ta Coronavirus a kasar ta Jamus sun haura mutum 1,570
Jami'ar ta Johns Hopkins na gudanar da nata binciken ne da ya sha bam-bam da na cibiyar Robert Koch Institut, ta kasar Jamus wacce tun daga farko ta ce za a iya samun adadi mafi karanci na wadanda suka kamu da cutar corona a yamacin lahadi.