1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta bunkasa tsaron kasarta

Suleiman Babayo LMJ
February 27, 2022

Gwamnatin Jamus ta dauki matakin karfafa harkokin tsaro tare da kara kashe kudi a bangaren tsaro inda aka sauya manufofin kasar kan yaki bayan farmakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.

Berlin | Sondersitzung zur Krise in der Ukraine
Hoto: Michael Sohn/AP/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya sanar da cewa kasar za ta kawa yawan kudin da take kashewa kan harkokin tsaro da fiye da kashi biyu cikin 100 na karfin tattalin arzikin kasar. A wannan Lahadi shugaban gwamnatin ya bayyana haka lokacin zaman na musamman na majalisar dokokin kasar ta Bundestag, kuma karfafa tsaron Jamus na da nasaba da kutsen da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, inda ya ce duniya ta shiga sabon lale.

Ya kara da cewa rundunar sojan Jamus za ta samu kudin Euro milyan dubu-100 kan zuba jari da samar da makamai daga gwamnatin tarayya. Olaf Scholz shugaban gwamnatin na Jamus ya ce daga yanzu duk shekara rundunar sojan za ta samu fiye da kashi biyu cikin 100 na duk karfin tattalin arzikin Jamus. Ita ma Annalena Baerbock Ministar harkokin wajen Jamus ta bukaci manyan kasashen duniya su ci gaba da matakan takunkuni kan Rasha yayin da Shugaba Vladimir Putin ya dauki matakin yaki.

A hannu guda kuma wakilan kasashen na Ukraine da Rasha na shirin haduwa domin su tattauna yiwuwar yin sulhu a tsakaninsu. Batun tattaunawar dai na zuwa ne, a daidai lokacin da shugaban Rasha Vladmir Putin ya baiwa rundunar sojojinsa umarnin sayan bangaren kula da makaman nunkiliya na rundunar da su zauna cikin shiri. A cewarsa ya dauki wannan matakin ne saboda barazanar kungiyar tsaro ta NATO da kuma takunkuman da kasashen Yamma da Amirka ke sakawa Moscow.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani