1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Wani matashi ya kashe kakarsa mai shekaru 100

Abdullahi Tanko Bala
September 7, 2023

Masu gabatar da kara sun ce matashin ya kashe kakar tasa ce saboda ya gaji da kula da ita. Ta rasu sakamakon rauni da ta samu a gadon baya

Jamus| Matashi mai shekaru 37 da ya kashe kakarsa
Hoto: Markus Scholz/dpa/picture alliance

Wani matashi dan kasar Jamus da ake zargi da kashe kakarsa mai shekaru 100 a duniya ta hanyar sararta da adda ya gurfana a gaban kotu a birnin Hamburg 

Matashin mai shekaru 37 da haihuwa ana tuhumarsa da aikata kisa sakamakon sarara da ya yi wa kakarsa a ranar 6 ga watan Maris.

Ba a baiyana sunansa ba karkashin dokokin kariyar bayanai ta Jamus. Sai dai an baiyana cewa dan asalin kasar Eastonia ne kuma haifaffen Jamus.

Takardar tuhumar da ake yi masa ta nuna shi ne yake kula da kakar tasa amma ya nuna kosawa da kula da ita a cewar masu gabatar da kara.

Matar wadda ke fama da matsalar gushewar hankali tana amfani ne da keken guragu, ya kuma kai mata sara a kanta har sau 16.

Wanda ake tuhumar shi ya kira yan sanda da kansa sannan ya mika kansa inda ya sanar da su cewa ya kashe kakarsa wadda ta riga mu gidan gaskiya a lokacin da yan sanda suka isa gidan.

Masu gabatar da kara sun ce a ranar litinin mai zuwa zai gabatar da bahasi a kotu a game da lafiyar kwakwalwarsa a lokacin da ya aikata laifin