1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Merkel ta bukaci a mutumta 'yan gudun hijira

August 28, 2020

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce idan da za ta sake samun dama za ta sake maimaita budewa 'yan gudun hijira kofa su shigo Jamus.

Frankreich Bormes-les-Mimosas | Fort de Bregancon | Pressekonferenz Angela Merkel
Hoto: Getty Images/AFP/C. Simon

Merkel ta ce ba ta yi nadamar budewa 'yan gudun hijira kofar shigowa Jamus a shekara ta 2015 ba. Merkel ta yi wannan karin haske ne yayin wani taron 'yan jarida na lokacin bazara da ta saba yi shekara-shekara. 

Shugabar ta ce idan da za ta sake samun dama za ta sake maimaita hakan. Ta kuma ce har yanzu tana da ra'ayin idan mutane sun zo iyakar Jamus da Ostriya ko iyakar Hangari da Ostriya a rinka kula da su a tamkar mutane. 

Wannan ra'ayin nata dai ya janyo mata farin jini a kasashen duniya. Sai dai a nan Jamus masu kyamar baki sun sha gwasale ta.