Jamus : Merkel ta wallafa littafin rayuwarta mai suna 'Yanci
November 26, 2024Littafin ya yi waiwaye kan abin da Angela Merkel ke tunawa lokacin mulkinta wanda aka yi wa suna "Yanci" ya bayyana a cikin harsuna 30 na duniya, inda zai zagaye manyan shagunan litattafai na kasashe da dama ciki har da kasar China. A kasar Jamus, tikitin shiga zauren da za a nuna littafin ya samu tagomashi a birin Berlin, domin an saye dukkanin tikitin, abin da ke nuna yadda har kawo yanzu Angela Merkel na da farin jini wajen Jamusawa.
Karin bayani : Merkel: Waiwayen baya da tsokaci kan Putin da Trump
Littafin mai adadin shafuka 736, a ciki Angela Merkel ta yi waiwaye daga shekarar 1954 zuwa shekara ta 2921, kama daga yanayin rayuwarta a tsohuwar kasar Jamus ta Gabas da sake hadewar Jamus ta Gabas da ta Yamma da fadi tashinta na siyasar Jamus tun daga lokacin har zuwa abubuwan da suka faru a mulkinta na shekaru 16. Don haka aka saka wa littafin suna "Yanci" Tunawa daga shekara 1954 zuwa 2021, an kuma fassari shi a cikin harsuna da ma na duniya. Baya ga haka, an dade ana shirya rangadin da Angela Merkel mai shekaru 70 da haihuwa za ta yi a manyan biranen Turai.
Karin bayani : Jamus ta karrama Merkel da lambar yabo
Gabanin kaddamar da littafin, wasu jaridu da mujallun Jamus sun tsegunta abubuwan da ya kunsa, kama daga batun yake-yake da rigin-gimun da duniya ke fiskanta tun daga yankin Gabas ta Tsakiya zuwa yakin Ukraine da Rasha, sannan kuma jaridun sun ce a cikin littafi, Angela Merkel ta bayyana huldarta da Donald Trump a wa'adin mulkinsa na farko a tsakanin 2017 zuwa 2021, da kuma yadda mazaje suka mamaye siyasar kasar Jamus, da cece-kucen da ya shafin karbar ‘yan gudun hijira a kasar, da kuma yadda huldarta ta kasance da Shugaban Rasha Vladimir Putin.