Jamus na ƙoƙarin shiga tsakani a rikicin Gabas ta Tsakiya
August 11, 2013Guido Westerwelle zai gana da shugaba Shimon Peres da kuma babbar minista mai shiga tsakanin ta ƙasar Tzipi Livini, kafin a gobe Litinin ya sadu da Firaminista Benjamin Netanyahu da kuma shugaban Palastinawa Mahamud Abbas,domin tattauna batun sake farfaɗo da shirin zaman lafiya. Bayan shekaru uku da shirin ya cije a rikicin da aka kwashe sama da shekaru 60 ana yi tsakanin ƙasashen biyu.
A watan da ya gabata na Yuli masu sasantawa na ƙasar wato Saeb Erkat da Tzipi Livini suka sake komawa kan teburin shawarwari tare da shiga tsakanin na Amirka. Nan gaba a ranar Laraba mai zuwa ce za a soma gudanar da wasu sabbin shawarwari tsakanin Yahudawan da Palastinawa a biranen Jerusalem da kuma Jeriko da ke a yankin Zirin-Gaza.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Edita Yahouza Sadissou Madobi