Jamus ta bijire wa yunkurin dawo da Rasha a G7
July 27, 2020Talla
Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas a cikin wata hirarsa da aka wallafa a safiyar Litinin din nan ya ce mamayar da Rasha ta yi wa yankin Crimea da tsoma bakinta a harkokin gabashin Ukraine suka sa aka fitar da ita daga cikin kungiyar G7 a shekara ta 2014, kuma har yanzu Rashan ba ta gyara wadannan kura-kurai ba.
A don haka Heiko Maas ya ce zai yi kyau idan Rasha ta gyara halinta kafin dawo da ita cikin kungiyar, yana mai cewa a baya-bayan nan Rasha ta hana isar kayan agaji zuwa ga mutane milyan daya da rabi da rikicin Siriya ya shafa. A saboda haka Jamus ta ce tana kira ga Rasha da ta daure ta zo a hada hannu domin shawo kan rikicin Siriya da Libiya da kuma Ukraine.