1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus na binciken harin Magdeburg

December 22, 2024

Ministar kula da harkokin cikin gida Nancy Faeser ta ce binciken zai duba irin matakan da jami'an tsaro suka dauka bayan gargadin da rahotanni suka ce an yi a kan dabi'un maharin tun a shekara ta 2023.

Hoto: Sebastian Kahnert/dpa/picture alliance

Gwamnatin Jamus na ci gaba da fadada bincike kan hakikanin abin da ya faru dangane da harin da wani dan kasar Saudiyya ya kai da mota a cikin kasuwar Kirsimeti ta garin Magdeburgda ke gabashin kasar. Ana sa ran 'yan sanda masu binciken muggan laifuka  za su bi diddigin yadda aka sarrafa bayanan gargadin da ake ce an samo a kan mutumin.

Kimanin mutane biyar ciki har da karamin yaro dan shekaru tara maharin ya halaka bayan da ya bi ta kansu da mota a ranar Juma'a da daddare. 

Mujallar Jamus ta Der Spiegel ta ruwaito cewa, shekara guda da ta gabata hukumomin leken asirin Saudiyya sun aike wa takwarorinsu na Jamus gargadi a game da dabi'un maharin, sai dai ba a dauki wani mataki a kansa ba.

Wannan lamari da ya jefa gaba daya Jamus cikin jimami tuni ya burkita wa 'yan siyasa lissafi, inda ya janyomatsin lambaga gwamnatin Olaf Scholz, yayin da ya rage watannin biyu a gudanar da zaben gabanin da wa'adi na 'yan majalisun dokoki ta Bundestag bayan da shugaban gwamnatin ya gaza tsalle kuri'ar yankar kaunar da 'yan majalisa suka kada masa a makon da ya gabata.