Jamus na cikin ruɗani a kan amincewa da Falasdinu
September 23, 2025
Kasashe da dama na yammacin Turai na son amincewa da yankin Falasdinu a matsayin kasa a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a wannan Litinin. Yayin da Jamus ba ta cikin kasashen, matsin lamba na karuwa a kan gwamnatin tarayyar dangane da haka.
A wannan Litinin din 22 ga watan Satumba wani babban al'amari zai wakana a birnin New York, a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya. Kasashen Faransa da Kanada da Belgium sun kudiri aniyar amincewa da yankin Falasdinu a matsayin kasa. Haka kuma Burtaniya ita ma akwai yiwuwar ta dauki wannan mataki.
Manufar ita ce kara yin matsin lamba a kan Isra'ila ta kawo karshen yakin Gaza da kuma kaddamar da sabon shirin zaman lafiya.
Daga cikin wakilan kasashe 193 na Majalisar Dinkin Duniyar, tuni kasashe kusan 150 suka amince da Falasdinun a matsayin kasa.
Amurka a daya hannun ta yi watsi da amincewar kamar yadda Isra'ila ita ma ta yi, inda Firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu ya bayyana matakin da cewa tamkar tukwici ne ga ta'addancin Hamas wadda Amurka da Isra'ila da kungiyar Tarayyar Turai da sauran su suka ayyana a matsayin kungiyar yan ta'adda, wadda ta kai hari kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 lamarin da ya haifar da yaki a Gaza.
Ga shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, amincewar irin wadannan manyan kasashe nasara ce gagaruma kuma kalubale ta diflomasiyya ga Isra'ila musamman yanzu da rikicin Gaza ke kara yin kamari.
Gwamnatin Jamus dai ba za ta dauki irin wannan mataki cikin kankanin lokaci ba kamar yadda Shugaban gwamnatin Friedrich Merz ya sanar a hukumance yana mai cewa ba su ga cikar sharudan kafa kasar Falasdinu ba a yanzu. Yace wajibi ne a matakin farko a amince da shirin zaman lafiya da zai samar da masalahar kafa kasashe biyu da za su zauna daura da juna.
Ga shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz wannan ba kalamai ne na fatar baki ba kamar yadda ya fada a lokacin sake bude wani wurin ibadar Yahudawa a birnin Munich.
Ya ce ''tun ranar 7 ga watan Oktoba, muke ganin karuwar kyamar Yahudawa da salo iri-iri, a furuci da kuma a aikace a kafofin sada zumunta; a jami'o'i da wuraren taruwar jama'a. Ina so in sanar da ku yadda wannan abu ya ba mu kunya ba kawai. A matsayina na shugaban gwamnatin Jamus, har ma da matsayina na Bajamushe wanda aka haifa bayan yaki, wanda ya taso da taken ba za a bari wannan abu ya sake faruwa ba wanda muka rike a matsayin alkawari."
Sai dai kuma a lokacin wata ganawa da ya yi da Firaministan Spain Pedro Sanchez a tsakiar wannan watan Merz ya yi tsokaci kan mawuyacin halin da al'ummar Gaza suke ciki yana cewa Insert.....
Ya ce "muna ganin tsananin wahalar da al'umma ke ciki a zirin Gaza. Mun yarda da hasashen cewa wannan bai dace da muradu na zahiri da aka yi tsammani daga gwamnatin Isra'ila ba. Amma bamu yarda da ayyanawar da aka yi cewa wannan mataki kisan kare dangi ba ne."
Gwamnatin dai na cikin tsaka mai wuya idan ana maganar Israila da kasar Falasdinu, sakamakon kisan Yahudawa miliyan shida a zamanin Nazi. A kan haka Berlin ke jin tana da nauyi da kuma hakki na tsaron Isra'ila wanda ya zama muhimmin jigo a kasar.
Sarkakiyar samuwar masalahar kasashe biyu da za su zauna daura da juna a yanzu babu alamar sa. Damar kafa kasar Falasdinu mai 'yancin cin gashinta da za ta zauna daura da Israila ta gushe tun fara yakin Gaza wanda ya hallaka mutane kusan 65,000 kamar yadda ma'aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta a Gaza ta nunar.
Wasu manazarta na ganin cewa gwamnatin Jamus ta gabatar da wannan bukatar ce mai kamar wuya a matsayin togaciya domin kau ce yanke hukunci kan matsayinta. Yayin da a waje guda ta ke fuskantar matsain lamba daga kungiyoyin farar hula a Turai ta dauki tsattsauran mataki akan Isra'ila ta hanyar sanya mata takunkumi.