1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yi tir da matakin Rasha

Zainab Mohammed Abubakar Rana Taha/SB
July 19, 2023

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta ce matakin da Shugaban Vladimir Putin na Rasha ya dauka na kin tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine zuwa ketare ya girgiza kowace kasa.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock tana hira da DW
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena BaerbockHoto: DW

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta ce matakin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya dauka na kin tsawaita yarjejeniyar hatsi da ke bai wa Ukraine damar fitar da hatsin da take nomawa zuwa ketare ya girgiza kowace kasa da kuma wakilan Majalisar Dinkin Duniya. Ta yi wannan tsokacin a Amirka.

Karin Bayani: Za a samu karancin abinci a duniya

A wata hira da ta yi da tashar DW a wajen bikin cika shekaru 25 da kafa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa wato ICC, a birnin New York na Amirka, Annalena Baerbock ta jaddada cewar ya zama wajibi Shugaba Putin ya ji kiran da duniya take masa na sake waiwayen wannan mataki nasa duba da yadda duniya ke cikin wadi na tsaka mai wuya na karancin ci-maka da yunwa da ke bazarana a wasu yankuna.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da Ines Pohl ta DWHoto: DW

"Kiran gama-gari na duniya da kiran da aka yi birnin New York a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Kowane wakilai daga kowace kasa ya yi mamakin ganin Putin ya sake dakatar da wannan shirin na hatsi, saboda mutane na iya jin yadda ake duniya ke matukar bukatar hatsi daga Ukraine a cikin watannin da suka gabata. Ya kasance ton miliyan 32 na hatsi zuwa kusan kasashe 45 na duniya. Sabili da haka yin amfani da wannan shiri da kuma amfani da yunwa a matsayin makami, dole ne mu ce bai dace ba. Sabili da haka, ana buatar matsin lamba a nan sosai. Matsin lamba a kan Rasha cewar, hatsi daga Ukraine na iya zagaya duniya."

Ministar harkokin wajen na Jamus ta ce, nauyi bai rataya a wuyan Turai kadai wajen yin matsin lamba a kan shugaban na Rasha ba, wajibi ne kasashe daga sauran nahiyoyi da suka hadar da na Afirka su hada karfi da karfe wajen ganin cewar cimma burin da aka sanya gaba na ceto duniya daga halin da take ciki:

"Na yi imani cewa mafi nasara shi ne cewa wannan kira ya fito daga kasashe Afirka, da Latin Amurka, da Asiya su yi magana da Putin kai tsaye. Mun gani a cikin shekarar da ta gabata cewa yana yin tasiri idan har sauran kasashe na duniya, ba kawai kawai kasashen Turai ba, suna kira ga Putin saboda yadda amfani da kasashe mafi rauni na duniya a yayin wannan yakin ta hanyar barin abincin ya isa izuwa garesu".

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena BaerbockHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A dangane da bukin cikar kotun ta ICC mai hukunta masu manyan laifuka na yaki shekaru 25 da kafuwa kuwa, Baerbock ta ce   har yanzu, alhaki ya rataya a wuuyanmu na karfafa dokokin kasa da kasa don hana yake-yae na gaba, don hana kisan kare dangi, laifukan cin zarafin bil'adama.

Jami'ar diplomasiyyar Jamus din ta jaddada mahimmancin tabbatar da cewa karin kasashe sun rattaba hannu kan yarjejeniyar Rome. A halin yanzu, kasashe 123 suka rattaba  hannu. Ta ce muhimmancin kotun ta ICC ya kara fitowa fili a cikin shekarar da ta gabata, a daidai lokacin da Rasha ke yaki da Ukraine.

Rasha dai na daya daga cikin kasashe biyar masu kujerar din din din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka fi sani da P5 tare da Amurka da China da Faransa da Birtaniya. Kuma tun a watan Maris ne kotun ta ICC ta bayar da sammacin kama Shugaba Vladimir Putin na Rasha saboda zargin da aikata laifukan yaki kan rawar da ya taka wajen korar kananan yara daga yankin da Rasha ta mamaye a Ukraine.