Jamus na duba yiwuwar sake kakaba dokar kulle
March 27, 2021![Berlin PK Gesundheitsminister Jens Spahn](https://static.dw.com/image/57011989_800.webp)
Talla
Hukumar da ke dakile yaduwar cutattuka ta kasar ta ce an sami sabbin masu dauke da cutar kimanin dubu 20 yayin da wasu dari da 5 da 7 suka mutu sanadiyar cutar a ranar Asabar, abin da ya sanya cibiyar Robert Koch ta yi gargadin cewa adadin ka iya haura hakan a nan gaba idan ba a dauki matakan da suka dace ba. Sai dai ministan ya ce za su tattauna don duba yiwuwar sanya dokar yayin bukukuwan Ista kamar yadda ta kasance a bara.