1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin jami'an soji ya addabi Jamus

April 2, 2023

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke son kara bunkasa rundunar sojinta yadda za ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana musamman ganin irin mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.

Hoto: Ints Kalnins/REUTERS

Rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr na fama da karancin jami'an da za ta tura fagen daga, a cewar kwamishiniya mai kula da harkokin soji a majalisar dokokin kasar Eva Högl.

Jami'ar ta ce ya kamata adadin sojojin Jamus ya kai 203,000 daga nan zuwa shekaru bakwai masu zuwa. A yanzu haka dai rundunar sojin ta Jamus na da jami'ai 183,000, da a cewar Högl, ba su wadata ba.

Hukumomi sun ce ficewar da kuratan soji ke yi daga rundunar ta Jamus da kuma matakai masu tsauri a wajen daukar sabbin kurata ne ke kara haifar wa Bundeswehr din karancin sojoji.