Jamus na fuskantar kamarin corona
October 17, 2020![Corona-Gipfel I Merkel und Ministerpräsidenten](https://static.dw.com/image/55283204_800.webp)
Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga 'yan kasar da su bayar da hadin kai da gaggawa domin ganin an dakile yaduwar cutar.
Da take magana a sakonta na mako mako, Merkel ta ce yana da kyau a dauki duk wasu muhimman matakan da suka dace wajen kawar da yaduwar cutar, kana ta bukaci takaita haduwar jama'a da dage duk wasu tafiye-tafiyen da basa da muhimmanci, tana mai cewa yanzu Jamus na cikin wani yanayi mai sarkakiya.