1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus na sake fuskantar barazanar corona

March 26, 2021

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Jamus sun yi gargadin cewa za a iya fuskantar babban kalubale a yaki da annobar corona a yanzu fiye da baya,

Berlin PK Gesundheitsminister Jens Spahn
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai a birnin Berlin, ministan lafiya na kasar Jamus Jens Spahn ya bukaci jama'a da su rage cudanya a yayin bukukuwan Ista da ke karatowa tare da gargadin cewa nan da 'yan makonni asibitoci ka iya cika da marasa lafiya saboda yadda annobar ke saurin yaduwa. 

Kazalika Spahn ya ce tuni gwamnati ta fara duba yiwuwar dakatar da zuwa hutu a wajen Jamus na dan wani lokaci, inda tuni ta kara tsaurara matakan tafiye-tafiye.