1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamus na taimaka wa Kwango gano masu fama da kyandar biri

Mouhamadou Awal Balarabe
August 21, 2024

Ministar raya kasa ta Jamus Svenja Schulze ta ce kasashen Afirka na nemon taimako don tinkarar kyandar biri, Saboda haka, kasarta na horas da jami'an kiwon lafiya dabarun gane alamomi kamuwa da Mpox a kasar Kwango.

Jami'an kiwon lafiya na kulawa da masu fama da kyandar biri a gabashin Kwango
Jami'an kiwon lafiya na kulawa da masu fama da kyandar biri a gabashin KwangoHoto: Zanem Nety Zaidi/Xinhua/IMAGO

Gwamnatin Jamus ta sanar da aika dakin gwaje-gwaje na tafi da gidanka zuwa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango don taimaka gano wadanda ke dauke da cutar kyandar biri.Fadar mulki ta Berlin ta kuma bayyana shirin horas da kwararrun jami'an kiwon lafiya dabarun gane alamomi kamuwa da Mpox da kuma sanar da jama'a matakan rigakafi. Ministar raya kasashe Svenja Schulze ta ce kasashen Afirka ne nemon taimakon duniya don tikarar cutar kyandar biri, kuma ya wajaba a kan Jamus ta ba da wannan taimako.

Karin bayani:  Kyandar biri: AU ta ce annobar na karuwa a Afrika

DR Kwango ce ke kan gaba a duniya wajen kamuwa da cutar Mpox da ma dai bullar wani sabon nau'i da ake kamuwa da shi cikin hanzari. Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana sabon  nau'in kyandar birin a matsayin abin damuwa kuma ta yi gargadin cewa yana iya yaduwa zuwa wasu kasashe. Cutar Mpox ba ta da saurin yaduwa kamar COVID19 kuma WHO ta ce ba ta tsammanin cewar za ta iya salwaantar da rayuwa ko dagula zamantakewar al'umma kamar yadda cutar sarkewar nunfashi ta yi.